MUSTAPHA ISHAQ ISMAIL

Magana nake akan madugun darikar kwankwasiyya, Bayan nasara da Allah ya bamu game da shari’ar da aka yanke hukunci a Abuja, naga wani video yana yawo na jawabinda madugu yakeyi dan gane da irin hukuncin da akayi, acikin bidiyo din yanacewa ALLAH YA TSINEWA WANDANDA SUKA ZALUNCESU KUMA XASU CIGABA DA TSINEWA WANDANDA SUKA XALINCESU.
Abin bai bani mamakiba tunda dama hausawa sunce GWANO BAYAJIN WARIN JIKINSA itadai wannan shari’a an riga an yanke hukunci baxanyi magana akanta ba, amma dole in tunawa magoya bayansa wadanda so ya hana ganin laifi irin zaluncin da madugu yayi tundaga lokacin gomnatinsa har zuwa yanzu dayake zagin masu mutunci.
A kwanakin baya SANATAN KANO TA TSAKIYA MAL IBRAHIN SHEKARAU yayi Hira a gidan radion kaduna acikin shirin (hannu dayawa) acikin shirin malam ya nuna takaicinsa gameda irin murkushewa da akeyiwa yan fansho a kasarnan, sannan ya bayyana cewa a lokacinda yabar gomnatin yabar kudi na yan fansho kimanin 9bn(biliyan tara) amma bayan yabar mulki da madugu yahau ya karkatar da kudin zuwa wani bangare inda su yan fansho suka koma yan kallo. YA MADUGU XAIYI DA TSINUWAR YAN FANSHO GAME DA HAKKINSU, kafin katsinewa wani kajida tsinuwarda talakawa sukeyima.
Bayan haka madugu yayi shirya zalunci lokacinda suka dawo jam’iyyar PDP suka tarar da mal Ibrahim Shekara da mutanensa wanda sune suka motsa jam’iyyar tun lokacinda ba’a iya tallatata. Zuwan madugu yayi karfa karfa ta hanyar hada baki da shugabancin jam’iyyar na kasa aka rushe tsohon shugabancin inda aka maye gurbinsa da magoya bayansa, hakan yasa malam shekarau yabar jam’iyyar dan nuna kishi ga magoya bayansa. YA XAKAYI DA TSINUWAR MAGOYA BAYAN SHEKARAU?
Bayan malam ya barmasa jam’iyyar wasu daga ciki sun biyo malam din wasu kuma sun zauna saboda suna tunanin madugu zaiyi musu adalci wajen fidda yan takara dukda basa sanya jar hula, Haka madugu ya shirya wani wasan kwaikwayo acikin daki da sunan (primary Election) ya tsayar da sirikinsa takara, duk da cewa akwa manyan yan siyasa wadanda ko takara suka tsaya da sirikin nasa baxaiyi nasara ba. Irinsu
1.Malam Salihu Sagir Takai
2.Hafizu Abubakar
3.Sadiq Aminu Wali
4.Muhammad Bello
Da dai sauransu amma haka madugu ya fidda dan takara son ransa ba tare da duba wa yayakeda rinjaye a jam’iyyar ba, hakan yasa wasunsu sukabar jam’iyyar don nuna fushinau, YA ZAKAYI DA TSINUWAR WADANNAN BAYIN ALLAH DA KAYIWA KARFA KARFA.
Amma duk da haka yanada bakinda zaice an cuceshi, da ikon Allah siyasarsa ce tazo karshe.
Amadadadin Ahalin mundubawa gidan malam shekarau muna addu’a Allah ya tsinewa wanda yayi sanadiyyar barinmu PDP. Amin
SHEKARAU FOR SENATOR
MUSTAPHA ISHAQ ISMAIL
21-01-2020
#SenIbrahimShekarauMedia


