SEN IBRAHIM SHEKARAU; AYYUKAN NAIRA MILIYAN DARI DA CASA’IN (190M).

SANATA SHEKARAU ZAI KASHEWA AL’UMMAR KANO TA TSAKIYA WATO KANO CENTRAL NAIRA MILIYAN DARI DA CASA’IN (190M).

Bisa koken Matsalar ruwa wanda wasu daga cikin Asibitoci dake Kano ta tsakiya suka kaiwa Mai girma Sanatan Kano ta tsakiya Malam Dakta Ibarahim Shekarau, tuni ya magance masu Matsalar, an fara Manya -Manyan Rijiyoyin Burtsatse masu amfani da Solar cikin wadannan Asibitoci ;

  1. Sabo Bakin Zuwo Maternity Hospital Jakara , Kano Municipal
  2. Sheikh Muhammad Jidda Hospital, Karamar Hukumar Fagge .
  3. Infectious Diseases Hospital, dake kan France Road .
  4. Yalwa bakin Kasuwa,Farawa, Karamar Hukumar Kumbotso, Wanda suma suke fama da rashin ruwa .
  5. Kasuwar Mayanka, Abbatuwa dake Karamar Hukumar Fagge.

GINA SABBIN AJUJUWA DA GYARARRAKI

Mai girma Sanata Ibarahim Shekarau ya fara aikin ;

  1. Gina Ajujuwa da abun Zama a Makarantar Wase Primary School dake Karamar Hukumar Minjibir .
  2. Tamburawa Primary School dake Karamar Hukumar Dawakin Kudu .

8 . Makarantar Islamiyya a Sabon Gida Bagujan , Karamar Hukumar Ungoggo

9 Bisa koken da Makarantar Mata ta Karamar Hukumar Kura ta Kai Ofishin Sanatan Kano ta tsakiya na rashin Dakin Dafa Abinci , an fara Gina Dakin Dafa abinci da Gina Katanga da Kofa da Gyaran dakunan kwanan Dalibai da Bandaki , duk a wannan Makaranta ta (Govt, Girls, Sec,Sch Kura)

10 Gina Babban Masallachi Na Salloli guda Biyar a Unguwar Rangaza dake Karamar Hukumar Ungoggo

wadannan Sabbin ayyuka za su lashe Kudi Naira Miliyan Dari da Casa’in (190M) a karkashin Ma’aikatar ayyuka da Gidaje ta Tarayya cikin ribar kafar ayyukan Sanatan Kano ta tsakiya Dakta Malam Ibrahim Shekarau na Shekarar 2020.

s4s.home.blog